Kungiyoyin Premier na rige rigen sayan yan wasa – Kwallon Kafa

Share it with your friends Like

Thanks! Share it with your friends!

Close

#LabarinWasanni #KallonKafa #HausaNews #HausaNewsSyndicate

Gasar lig-lig ta kasashen Turai ta 2018-2019 ta kawo karshe kuma tuni kungiyoyin suka fara mayar da hankali kan kakar badi ta 2019-2020.
A ranar Alhamis 16 ga watan Mayu aka bude kasuwar saye da musayar ‘yan wasan ta bana, wadda za ta kai har zuwa ranar 8 ga watan Agusta.
Kocin Man United Ole Gunnar Solskjaer ya amince cewa “yana bukatar sabbin ‘yan wasa” bayan sun kare a mataki na shida da maki 32 a kasan zakarun gasar Manchester City.
Chelsea ba ta san matsayinta ba har yanzu
Eden HazardHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image caption
Hazard ka iya koma wa Madrid a kyauta idan har ya kai karshen kakar badi a Chelsea
Kungiyar Chelsea tana jira ta san matsayinta game da hukuncin da aka yi mata na haramcin sayan ‘yan wasa kuma kusan komai ya dogara ne kan daukaka karar da ta yi.
Samun damar buga gasar Champions League ya saka ta a tsaka-mai-wuya.
Rahotanni na cewa sun yi niyyar karbar hukuncin kafin su samu damar, amma yanzu suna bukatar kwararrun ‘yan wasa don neman lashe kofin gasar mafi girma a nahiyar Turai.
Sai a watan Yuli ne za a saurari daukaka karar, inda ake sa ran idan sun yi nasara za su bar Eden Hazard ya tafi Real Madrid.
Idan kuwa akasin haka ta faru to za su gwammace su rike shi, ganin cewa Pedro da Willian sun fara cimma shekarun tsufa – dukkaninsu sun shiga shekara 30 kuma Higuin yana a matsayin aro ne a kungiyar, inda shi kuma Giroud kwantiraginsa ke karewa.
Har wa yau, idan ba su sayar da shi yanzu ba to kwantiraginsa zai kare a karshen kakar badi, wanda hakan ke nufin zai bar kulob din a kyauta ke nan.
Manchester United
Jadon SanchoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image caption
Farashin Jadon Sancho dan wasan gaban Dortmund zai iya kai wa fam miliyan 100
Man United na yunkurin shigo da manya kuma matasan ‘yan wasa cikin kungiyar.
Inda suka fi tsananin bukatar sauyi shi ne ‘yan wasan baya da tsakiya da kuma ‘yan gaba masu buga gefe.
Babban dan wasan da suke hankoron dauka shi ne Jadon Sancho mai shekara 19, wanda Real Madrid da Barcelona da PSG duka ke nema.
Daga cikin zabinsu akwai Kalidou
Man United za ta fafata da Man City wajen daukar Koulibaly
Dan shekara 27, Koulibaly yana da sauran kwantiragin shekara uku da kungiyarsa ta Napoli, wanda za ta kare a shekarar 2023 kuma farashinsa zai kai akalla Yuro miliyan 150 da ke kunshe a yarjejeniyarsa ta 2021.
United za ta yi gogayya da abokiyar hamayyarta Man City wajen sayan dan wasan baya Wan-Bissaka, sannan kuma ga Rabiot dan wasan tsakiyar PSG duk da cewa hakan ya dogara ne ga abin da ya faru da Paul Pogba, wanda ake alakantawa da Real Madrid.
Arsenal na neman dan wasan baya da tsakiya
Aaron Ramsey
Tun tuni Aaron Ramsey ya kulla yarjejeniya da Juventus kuma da shi za a fara kakar badi a Italiya
Ganin ta samu damar shiga gasar Europa, Arsenal za ta nemi wanda zai maye gurbin Ramsey kuma ana tsammanin za su kashe kimanin fam miliyan 40.
Amma ana sa ran idan ta lashe kofin Europa, wanda zai ba ta damar buga Champions League kasafin kudin zai fi haka.
‘Yan wasan da suka fi nema su ne masu buga baya da kuma dan wasan tsakiya mai shige da fice daga raga zuwa raga.
Rahotanni sun nuna cewa suna neman dan wasan bayan Getafe Djene Dakonam, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a 2021 kuma yake da farashin fam miliyan 13.

Comments

Write a comment

*